DW ta kaddamar da shirin talabijin a harshen Turanci | Siyasa | DW | 22.06.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

DW ta kaddamar da shirin talabijin a harshen Turanci

"Muna son bai wa masu kallon tashar labarai na bazata, wato za mu rika basu labarai na burgewa. Inda mai sauroro zai ce kai wannan labarin na DW ban taba jin shi ba"

GMF 2015 Media Summit If it bleeds, it leads

Mahalarta taron koli na kafafan yada labarai (GMF 2015)

Daga ranar Litinin din nan 22 ga watan Yuni, DW za ta ci gaba da yada labarai ta talabijin a harshen Turanci, da sauran shirye-shirye tsawon sa'o'i 24 kowace rana.

Wannan shi ne jigo ciki shirin da tashar ta kaddamar a baya-bayan yayin taron koli na kafafan yada labarai na duniya (GMF 2015), nan kuma gagarumar nasara ce ga babban daraktan DW Peter Limboug domin shi burin da ya sa gaba tun fara aiki shekaru biyu da suka gabata kamar yadda ya yi karin haske.

"Mu sannanu ne, kuma kasashen duniya za su rika gwada kwarewarmu ta aikin jarida bisa ayyukanmu. Kuma mun yi imanin cewa bukatar da masu sauraro ke da ita a DW tana da yawa, don haka a sabbin shirye-shiryen za mu iya daga nan Jamus mu bayar da bayanan fiye da a da"

GMF 2015 Eröffnung Peter Limbourg Sendestart

Shugaban DW Peter Limbourg a dama daga gaba

A sabon shirin na sa'o'i 24 ba kakkautawa, kusan ko wane sa'a ana rika sabunta labaran. Nahiyoyin Turai, da Latin Amirka za su samu matukar kulawa. Amma fa nahiyoyin Afirka da Asiya su ne kan gaba. Hakan na yasa DW ta fadadad masu nemo mata labarai. Inda a yanzu wakilai kama daga Biranen Bangkok, izuwa Lagos da Kairo za su rika aiko da rahotanni. Carsten von Nahmen shi ne daraktan yada labarai a tashar DW:

"Muna son bai wa masu kallo tashar labarai na bazata, wato za mu rika basu labarai na burgewa. Inda mai sauroro zai ce kai wannan labarin na DW ban taba jin shi ba, ko kuma mai kallo rika cewa dana kalli tashar DW na karu"

Yayinda ake fara sabon shiri haka kuma aka gina sabon dakin watsa labaran, inda injiniyoyi suka dau lokaci suna aiki ba kama hannun yaro. Wade Adams na cikin masu lura da aikin.

"Dakin yada labaran babbane, kuma muna iya yin komai cikin sauki. Akwai na'urorin da za su bamu damar inganta hutonanan kan shirin da muke don burge mai sauraro"

A cewar Babban Daraktan tashar DW, manufarsu a sabon shirin Talabijin shi ne, daukar masu kallon labaran da mahimmanci, kula da al'adu da kare hakkin jama'a, domin kwadaitar da mutane kan al'amura da ke faruwa duniya.

Sauti da bidiyo akan labarin