DW: Sashen Turkanci na YouTube | Labarai | DW | 29.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

DW: Sashen Turkanci na YouTube

An kaddamar da tashar You Tube da harshen Turkanci karkashin jagorancin tashar DW da sauran tashoshin yada labarai na kasashen duniya inda za ta dinga yada shirye-shiryenta daga Turkiyya.

Tashar DW da wasu tashoshin yada labarai na kasa da kasa sun hada hannu wajen kaddamar da tashar YouTube ta harshen Turkanci mai suna +90, da nufin karfafa 'yancin fadan albarkacin baki da na kafafen yada labarai a Turkiyya. Yayin da yake zantawa da manema labarai a gefen taron kaddamar da tashar, shugaban tashar DW Peter Limbourg ya yi karin haske kan wadanda suke fatan za su rinka sauraro da kuma kallon tashar yana mai cewa "wadanda muke son mu isa gare su za su kasance ne matasa 'yan tsakanin shekaru 18 zuwa 35 a duniya, muna son mu samar musu da wata dama ta tattauna duk wasu batutuwan da suke iya tattaunawa domin cimma wani burinsu. Amma ko baya ga matasan duk wadanda ke da sha'awa za su iya kallonmu Shugaban tashar DW Peter Limbourg ya bayyana cewa a Turkiyya ana amfani da YouTube sosai saboda haka ina ganin za mu samu masu kallonmu sosai.