1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ivan Duque ya zama zababben shugaban Kwalambiya

Suleiman Babayo MNA
June 18, 2018

Ivan Duque mai ra'ayin mazan jiya ya lashe zaben kasar Kwalambiya zagaye na biyu inda ya doke Gustavo Petro.

https://p.dw.com/p/2zkzz
Kolumbien Ivan Duque in Bogota
Hoto: Getty Images/AFP/P. Arboleda

Sakamakon zaben Kwalambiya ya nuna cewa Ivan Duque mai ra'ayin mazan jiya ya lashe zaben da kashi 54 cikin 100, inda ya kada mai kalubalantansa Gustavo Petro.

Zababben Shugaban Ivan Duque dan shekaru 42 da haihuwa ya kasance mafi karancin shekaru da ya shugabanci Kwalambiya a cikin fiye da shekaru 100 da suka gabata, kuma ya yi alkawarin hada kan 'yan kasar duk da yana nuna dari-dari kan kalaman suka da yake yi kan shirin zaman lafiya na kasar.

A watan Agusta mai zuwa Ivan Duque zai dauki madafun ikon kasar ta Kwalambiya da ke yankin Latin Amirka.