1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya za ta taimaka wa Kenya a kan tsaro

June 28, 2014

Majalisar Dinkin Duniya na shirin taimaka wa Kenya yakar ayyukan ta'addancin da ke addabarta, sakamakon neman zama ruwan dare da hare-hare ke yi a kasar.

https://p.dw.com/p/1CS6D
Hoto: Reuters

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya bayyana cewar hukumar da ya ke shugabanta ta kudiri aniyar taimaka wa Kenya kawo karshen ayyukan ta'addancin da ke addabarta. A lokacin da ya yi wannan bayanin a Nairobi bayan da ya gana da shugaban kasar Kenya, Mista Ban ya ce tuni suka tattauna da Uhuru Kenyatta kan irin gudunmawar da majalisar za ta bayar, ba tare da ya yi karin haske ba.

Hare-haren bama-bamai na neman zama ruwan dare a Kenya tun bayan da gwamnatin wannan kasa ta tura da sojojinta Somaliya a 201, don yakar 'yan al-Shabaab da ke tayar da kayar baya. Ita wannan kungiyar ce ta dauki alhakin mummunan harin nan na Westgate da ya hallaka mutane 61, da ma na garuruwan da ke kusa da gabar ruwan kasar ta Kenya, wadanda suka lamshe rayukan mutane kimanin 70.

Sai dai shugaban Kenyatta ya karyata ikirarin da al-shabaab ta yi na kai hare-haren, inda ya dangantasu da wani mataki na abokan gabansa na siyasa da nufin shafa wa gwamnatinsa kashin kaji.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Usman Shehu Usman