Duniya za ta taimaka wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya | Labarai | DW | 26.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Duniya za ta taimaka wa Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya

Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce akwai buƙatar gaggawa ta samar da zaman lafiya a ƙasar da ta ba da izinin tura dakarunta kusan dubu shida domin yin aikin tabbatar da tsaro.

Faransa ta ce a shirye ta ke ta aike da ƙarin sojoji 800 a Jamhuriyar ta Afirka ta Tsakiya da ke fuskantar wani mummunar halin na tashin hankali. Wanda ƙasashen duniya suka bayyana fargabnsu a kan ta'addin da ake tafawa na aikata kisan gila da fyaɗe akan al'ummar ƙasar. Mataimakin sakataran MDD Jan Eliasson ya ce tilas ne a ɗauki matakai na gaggawa domin magance abubuwan na asha da ke faruwa a ƙasar.

A wani zaman da kwamitin sulhu na MDD ya yi a jiya, Faransa ta ce za ta ajiye wani daftari ƙudiri a gaban majalisar na sake dawo da doka a ƙasar da ta faɗa cikin ruɗani da rashin tabbas.Tun bayan juyin mulkin da ƙungiyar 'yan tawaye ta SELEKA a ƙarƙashin jagorancin , Michel Djotodia ta yi wa Francois Bozize a cikin wata Maris da ya gabata.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Usman Shehu Usman.