1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya ta yi maraba da sabuwar shekara 2014

January 1, 2014

An gudanar da bukukuwan shigowar sabuwar shekara ta 2014 Miladiya cikin sassa daban-daban na duniya

https://p.dw.com/p/1AjyI
Hoto: Getty Images

An gudanar da shagulgular tarbar sabuwar shekara ta 2014 cikin birane daban-daban na duniya, kama daga birnin Sydney na kasar Australiya, da Seoul na Koriya ta Kudu ta Kudu, da Tokyo na kasar Japan, da biraranen kasashen Turai da New York na kasar Amirka.

Miliyoyin mutane suka kalli wasannin wuta da aka gudanar a birane daban-daban daga gabashi zuwa yammacin duniya.

A cikin sakon Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel kan sabuwar shekarar, ta nemi Jamusawa su kara zage damtse domin cimma manufofin da aka saka a gaba cikin wannan shekara ta 2014.

A birnin New York na kasar Amirka jim kadan da shiga sabuwar shekarar aka rantsar da magajin garin birnin Bill de Blasio, kuma wani lokaci da ranar yau ake gagarumin bikin kaddamar da magajin garin, bayan wannan rantsuwa ta fara aiki, inda ya ce zai ci gaba da aikin rage laifuka a birnin, da cike gibin da ke tsakani masu arziki da matalauta.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Umaru Aliyu