1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Duniya ta yi ca kan Trump saboda sauyin yanayi

Aliyu Muhammad Waziri
June 2, 2017

Duniya na cigaba da mai da martani dangane da sanarwar Shugaban Amirka Donald Trump na ficewa daga yarjejeniyar kare muhalli ta birnin Paris wadda duniya ta amince da ita.

https://p.dw.com/p/2e35V
USA Trump verkündet Ausstieg aus Pariser Klimaschutzabkommen
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Shugaban ya bada wannan sanarwa ce da yammacin Alhamis, sai dai duk da ficewar Amirkan wasu na ganin za a kai ga cimma nasarar da ake bukata na kare muhallin.

Tun bayan bayyana shirin ficewar Amirkan da Shugaba Donald Trump ya yi dai, tuni kasashen duniya suka yi ca wajen yin Allah wadai da wannan yunkuri na shi, duk da cewa shugaban ya bayyana cewar akwai yiwuwar kasar ta sake komawa cikin yarjejeniyar nan gaba in har ta dace da bukatar Amirka. Yanzu haka dai jama'a da dama a kasar ra'ayin su ya banbanta dangane da matakin, yayin da wasu ke goyon baya wasu ko akasin haka ne.

Angela Merkel PK Klimaabkommen
Hoto: Reuters/F.Bensch

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi Allah wadai da matakin ficewar Amirkan tare da cewa ficewar Amirkan ba zai hana su cigaba da taimakon duniya ba wajen ganin an kare muhalli daga mummunan yanayin da ya ke ciki ba:

"Matakin Amirka na ficewa daga yarjejeniyar kare muhalli ta Paris, abin takaici ne matuka, don haka ina mai kara jaddada cewa muna tare da wannan yarjejeniya babu gudu babu ja da baya. Wannan yarjejeniya dai ita ce mafi girma kan kare muhalli da duniya ta cimma wadda ake sa ran nan da shekarar ta 2030 lamura za su dai-daita. Ya zama wajibi a garemu da mu fuskanci gaba. Don haka wannan abu lallai ba za mu bari ya sanyaya mana gwiwa ba wajen tabbatar da mun kare duniya ba."

Kungiyar Tarayyar Turai ma ta mayar da martani kan wannan batu ta bakin shugaban hukumar hadin kan Turai  Jean Claude Juncker:

"Babu gudu babu ja da baya dangane da gyaran da muke son kawowa. Babu wani abin da zai sa mu janye daga yarjejeniyar Paris, domin duk wani abin da muke yi, ya dogara ne bisa ga aiki tukuru ba tare da boye-boye ba, kuma muna aiki ne bisa ga dokar kasa da kasa."

USA Umwelt Proteste gegen Trump in Washington DC
Hoto: picture-alliance/ZUMAPRESS.com

Cikin wani taron manema labarai da ma'aikatar harkokin wajen Indunusiya ta kira da safiyar wannan Juma'a, mai magana da yawun ma'aikatar Arrmanatha Nasir ya bayyana cewa lallai ficewar Amirkan baya daga cikin yarda da amincewa da duniya baki daya ta yi amanna da su cewa su ne za su kai duniyar ga tudun na tsira.

Sai dai a nashi bangaren Shugaba Donald Trump ya yi amanna da cewa yarjejeniyar ta Paris baya ga asara da durkusar da tattalin arzikin Amirka babu wani abu mai amfani da take ga kasar, don haka ne ma yake ganin ficewar ita ce mafi a'ala ga cigaban kasar.