Duniya ta yi Allah wadai da harin Baga | Labarai | DW | 14.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Duniya ta yi Allah wadai da harin Baga

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna kaduwarta bisa kisan dubban mutane a arewacin Najeriya, inda ta bukaci gwamnati ta dau matakin magance matsalar

A cewar MDD rikicin Boko Haram na zubar da jinin bayin Allah a arewa masu gabacin kasar. Hukumar kare yancin dan Adam ta Majalisar, ta bada rahoton cewa sama da mutane dubu 11 suka tsallaka daga Najeriya izuwa kasar Chadi, biyo bayan harin da kungiyar ta kai kwanakinnan. Kakakin hukumar ya ce a harin da kunkiyar Boko Haram ta kai Baga, dagangan suka yi ta hallaka fararen hula, abinda kuma ya sabawa dokar kasa da kasa. MDD ta ce abun damuwa ne yadda aka bada rahoton yi wa yara kanana da tsaffi kisan ba gaira. Inda kakakin ya kara da cewa harin da aka kai a kasuwar Maiduguri da Pataskum abubuwa ne na kaduwa. Majalisar ta Dinkin Duniya, ta bukaci gwamnatin Najeriya ta gaggauta maido da doka da oda, kana ta tabbatar sojojinta suna aiki bisa ka'idojin da kasa da kasa suka amince da su, su mutunta yancin dan adam.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Umaru Aliyu