1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zangar kin jinin manufofin gwamnati

Binta Aliyu Zurmi
September 3, 2023

Dubban al'ummar kasar Isra'ila sun kara fantsama titunan birnin Tel Aviv da wasu manyan garuruwan kasar suna masu yin tir da sabbin manufofin gwamnatin Shugaba Benjamin Natenyahu.

https://p.dw.com/p/4VtId
Israel Tel Aviv | gewaltsame Proteste von eritreischen Asylbewerbern
Hoto: Ilia Yefimovich/dpa/picture alliance

Wannan na zuwa ne bayan duk a jiya Asabar aka yi taho mu gama tsakanin 'yan ciranin kasar Eritrea da ke zaune a kasar da kuma 'yan sanda.

Gwamman mutane ne masu aiko da rahotanni suka tabbatar da cewa sun jikkata bayan arangamar da ta barke tsakanin jami'an tsaro da masu bore.

Kasar Isra'ila ta kwashe sama da watanni 6 tana fuskantar fushin al'umma tun bayan da wannan gwamnatin ta bijiro da wasu sauye sauye a fannin a dokokin sharia'ar kasar.

Lamarin da dama ke sukar shi , inda wasu ke cewar yana zama wata babbar barazana ga mulkin dimukradiyyar kasar.

A ranar 12 ga watan Satumba nan ne kotun kolin kasar za ta yi zama a kan karar da aka shigar don duba wannan doka da aka yi wa garanbawul.