1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dubban yan Afirka sun yi zanga-zanga a Tel Aviv

January 5, 2014

Bakin haure 'yan Afirka dake fuskantar barazana a Isra'ila ne suka nuna rashin jin dadin su ga dokokin Israila na kin amincewa dasu a matsayin yan gudun hijira

https://p.dw.com/p/1AlaJ
Hoto: Reuters

Fiye da mutane 30.000 ne 'yan asalin kasashen Afirka suka gudanar da wata zanga-zangar lumana a wannan Lahadin a birnin Tel-Aviv na kasar Isra'ila. Masu zanga-zangar dai sun shiga kasar ta Isra'ila ne ta barauniyar hanya. Wannan dai shi ne wani babban taron gangami irin haka da aka gani cikin wannan kasa a cewar wata majiya ta yan sanda. Masu zanga-zangar na nuna rashin jin dadinsu ne ga halin hukumomin kasar na kin kula da duba halin da suke cikin a matsayinsu na wadanda suka yi gudun hijira, sannan da dakatar da wasunsu da hukumomin kasar suka yi, inda suke cewa mu duka 'yan gudun hijira ne, a bamu 'yancinmu, kuma a daina rufe mu a gidajan kaso, wadanda akasarin su sun daga tutar kasar Eritreya da ta Habasha.

Mawallafi: Salissou Boukari
Edita: Umaru Aliyu