Dubban mutane na neman mafaka a Siriya | Labarai | DW | 07.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban mutane na neman mafaka a Siriya

Sojojin hada ka tare da tallafin mayakan sa kai suna ci gaba da fatattakar mayakan jihadi masu alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda a Siriya lamarin da ya haifar da dubban 'yan gudun hijira masu kauracewa gidajensu.

Akalla mutane dubu 152 000 ne a cikin mako guda suka kaurace wa gidajensu domin samun mafaka a kudancin Siriya kamar yadda Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana, sakamakon tsawaitar hare-hare ta kasa da ruwan Bama-bamai da dakarun sojan Siriya hadin gwiwa da abukanin huldarsu na kasar Rahsa ke kai wa yankunan da ke hannun mayakan kungiyar jahadin nan mai alaka da kungiyar Alq'ida.

Farmakin dai ya raunata wasu fararen hula da dama a tsakanin 29 ga watan Aprilu zuwa biyar ga watan Mayu a cewar hukumar bayar da agaji ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA.

Duk da kawo karshen kungiyar mayakan jihadi na kungiyar IS da kawancen kasashen duniya suka yi a Siriya, har yanzu tsugunne bata kare ba domin wasu yankunan kasar sun gagari dakarun gwamnati da kawayenta wadanda yanzu hakan suke hannun Hayat Tahrir al-Cham ( HTS ) a takai ce mai goyon bayan al'ka'ida.