Dubban mutane na kaurace wa gidajensu a Nijar | Labarai | DW | 09.04.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dubban mutane na kaurace wa gidajensu a Nijar

Fiye da mutane 18,000 ne aka tilasta masu barin muhallansu a Jamhuriyar Nijar bayan da mayakan Boko Haram suka zafafa hare-hare kamar yadda Hukumar kula da 'yan gudin hijira ta MDD (UNHCR) ta bayyana a wannan Talata.

Niger Flüchtlinge aus Nigeria (DW/A. Cascais)

Mata da yara kan tsinci kai a hali na tsaka mai wuya bayan harin Boko Haram

Kimanin fararen hula 88 ne rahotanni a watan Maris suka nunar da cewa an halaka su a yankin kudo maso gabashi na kasar da ke da yawan Sahara, adadin da ke da yawa idan aka kwatanta da jumullar wadanda aka halaka 107 a shekarar bara.

Babar Baloch da ke magana da yawun Hukumar kula da 'yan gudun hijirar ta MDD ya fada wa manema labarai a birnin Geneva cewa, abin takaici ne yawan adadin mutane da ke rasa rayukansu duk wata wadanda ba su ji ba ba su gani ba. Da dama dai mutanen da ke gujewa hare-haren na Boko Haram na fakewa a yankin Diffa.