Dubban mutane ke mutuwa kowace shekara a duniya sakamakon sarar maciji | Zamantakewa | DW | 19.09.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Dubban mutane ke mutuwa kowace shekara a duniya sakamakon sarar maciji

Bincike ya nuna akalla mutane miliyan biyu da dubu 700 kan fuskanci matsalar sarar maciji, inda daga ciki akalla dubu 100 kan rasa rayukan su kowace shekara.

To wannan matsala ta sarar maciji dai tun ba yau ba al'ummomin kasashen duniya musamman a nahiyar Afrika ke fama da ita, kuma ma akasari al'ummar karkara daga cikinsu manoma, sun fi fuskantar wannan matsala ta cizon maciji. A dangane da wannan matsalar ce jami'ar Jos da ke Najeriya ta yi wani bincike inda ta samo wani magani na rigakafin cizon maciji da ake kira KOBIPLUS kamar yadda Farfessa Abraham Dogo ya yi karin haske kan binciken.

"Wannan maganin rigakafi ne na kowane irin nau'i na maciji, kamar irinsu gobe a nisa a nan Najeriya wanda ya ciji mutunm cikin sa'o'i 24 ya rasu. Wannan magani na tafi da gidanka, wato za ka iya sakawa cikin aljihunka ko da rana ta kan baci."

Ana amfani da dafin macizai dabam-dabam don samar da sinadaran magungunan rigakafi

Ana amfani da dafin macizai dabam-dabam don samar da sinadaran magungunan rigakafi

Wani bincike ya gano akasarin lokuta wadanda macijin kan sare su kan rasa rayukansu ne sakamakon rashin samun magani cikin gaggawa. To sai Farfessa Aboi Madaki na jami'ar Jos ya ce sun samar da allurar rigakafin cizon macijin da za a yi wa manoma da sauran jama'a tun kafin maciji ya sare su don kiyayewa.

A bangare guda kuma, masu maganin gargajiya suma dai suna ba da gagarumar gudummawa wajen shawo kan wannan matsala ta cizon maciji, inda fitattun likitocin gargajiya irin su Dr. Hammanjulde Gashaka suka yi fice wajen maganin cizon maciji. Ya kuma yi karin haske na na'uin macijin da suka fi shan wahalar jinyarsa a Najeriya.

"Kububbuwa shi ya fi ba da wahala, shi ne kuma ya fi yawa a Najeriya. Da ya sari mutum cikin mintuna 30 dafinsa ya riga ya zagaye jikin gaba daya.

To a yayin da duniya ke kiyaye wannan rana ta sarar maciji don ilmantar da al'umma kan wannan matsala, masana sun kawo shawarar kafa wasu karincibiyoyin jiyyar sarar maci, musamman a yankunan karkara tare ma da sansanonin 'yan gudun hijira da ke sassan dabam-dabam na Najeriya don magance wannan matsala ta sarar maciji da kan yi sanadiyyar rasa rayukan al'umma da dama.

Sauti da bidiyo akan labarin