Dubban Musulman Myanmar ke tserewa tashin hankali
September 1, 2017A cewar hukumomin kasar akalla mutane 400 suka mutu a jihar Rakhine, inda rikici ya barke bayan da masuadawa kuncin rayuwar da kabilar ke fiskanta, suka kai harin wa jami'an tsaro. Sai dai 'yan kabilar ta Rohingya da yanzu ke ciki ugubar dakarun gwamnati, sun musanta ikirarin da aka yi cewa su ne suka fara kai hari wa jami'an tsaro. Kamfanin dillalcin labarai na AP ya ruwaito cewa dubban musluman 'yan kabilar ta Rohingya, aka ga suna ta isa Bangladesh a kafa, tsaffin da basa iya tafiya wasu an goyesu, yayin da aka ga yara na goye da jarirai. Mutanen dai basa dauke da komai illa tsumakaransu, inda suka bayyana cewa sun yi tafiyar akalla kwanaki uku kafin su isa kan iyakarsu da kasar Bangaldesh. Akallla dai akwai 'yan Rohingya da ke cikin ugubar rayu, bisa cin zali da gwamnati ke yi musu, kuma har yanzu hukumomin Myanmar basa yardan cewa yan kabilar ta Rohingya a matsayin yan kasa ne ba.