1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango rikici na kara ta'azzara

Mouhamadou Awal Balarabe AMA(SB)
May 27, 2022

A lardin Kivu na arewacin Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango, an shafe kwanaki ana artabu tsakanin sojojin kasar da 'yan tawayen M23 da ke da goyon bayan Ruwanda.

https://p.dw.com/p/4ByRp
DRC | Ayarin sojoji dauke da makamai
DRC | Ayarin sojoji dauke da makamaiHoto: Alain Uaykani/Xinhua/picture alliance

Sojojin Kwango sun gano wasu makamai da 'yan tawayen M23 suka yi watsi da su, bayan da aka fatattake su daga yankin Rutshuru da ke gabashin kasar. Dama dai fadan da ya sake barkewa ya kai yankin Nyiragongo da ke makwabtaka da Goma, babban birnin lardin Kivu ta Arewa. Tun karshen shekarar da ta gabata ne 'yan tawayen wadanda akasarinsu 'yan kabilar Tutsi ne ke zargin hukumomin Kinshasa da rashin mutunta alkawurran da suka yi musu.

Sai dai Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango ta farfado da tsarin kula da ci gaban yankin tare da sa ido kan yarjejeniyar zaman lafiya da tsaro. Laftanar Janar Sylvain Ekenge, kakakin gwamnan soji na arewacin Kivu, ya ce makaman da wannan tsari ya bankado sun fi karfin 'yan tawaye. "Wadannan makaman sun hada da roka mai tsawon mm 60 da bindigar AK 81 da rokokin tanka guda takwas, da harsashi na PKM da kakin soja guda biyu da hular kwano da tulun shan ruwa ma sojoji guda biyu, wanda ba na rundunar sojin Kwango ba ne kuma ba na 'yan ta’addar M23 ba ne."

Karin Bayani: 'Yan tawayen M23 sun hada fada a Kwango

Wadannan makamai sun sa sojojin Kwango kara tabbatar da zargin da suke yi kasar Ruwanda cewa tana da hannu dumu-dumu a wannan rikici, sai dai kasar Ruwanda ta sake musanta zargin da Kwango ke mata na mara wa 'yan tawayen M23 baya, kana a nasu bangaren, 'yan adawa na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango sun yi tir da abin da suka kira harin wuce gona da iri da aka kai wa kasarsu. Ko da jam'iyyar siyasa ta ECIDE da ke karkashin jagorancin Martin Fayulu, ta ce tana shirin gudanar da zanga-zanga don nuna goyon baya ga sojojin kasarsu, a cewar Jean-Baptiste, dan majalisa da ake zama karkashin jam'iyyar ECIDE.

 Wannan dai ba shi ne karon farko da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kwango ke zargin Ruwanda da goyon bayan 'yan tawaye daban-daban a gabashin kasar ba. Sai dai ‘yan watannin da suka gabata, shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya yi barazanar tura dakarunsa domin fatattakar abokan gabarsa a gabashin Kwango. Dangantaka tsakanin Kwango da Ruwanda ta yi tsami tun bayan kisan kiyashin da aka yi a Ruwanda a shekarar 1994. musamman ma bayan da 'yan Hutu da ake zargi da neman murkushe 'yan Tutsi suka samu mafaka a Kwango