Dolene Ruto ya halarci zaman Kotu | Labarai | DW | 25.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dolene Ruto ya halarci zaman Kotu

A yayin da mahukuntan kasar Kenya da kungiyar hadin kan Afirka ke neman a dage sauraron tuhumar da ake yiwa shugabannin kasar Kenya a kotun ICC, kotun ta ce dolene Ruto ya halarci zamanta.

Kotun hukunta masu aikata manyan laifuka ta kasa da kasa wato ICC tace dole ne mataimakin shugaban kasar Kenyan William Ruto, ya halarci dukkan zaman kotun yayin tuhumar da ake masa ta aikata laifukan yaki.

Alkalan kotun ta ICC ne suka sanar da hakan, bayan wani zama da alkalan daukaka kara suka gudanar a yau Jumma'a, inda suka ce kuskure ne hukuncin da aka yanke a watan Yulin da ya gabata wanda ya baiwa Ruto, damar kin zuwa kotun a zaman ta daban daban da ta gudanar kan tuhumar tasa.

Sai dai kuma alkalan sun amince cewa za a iya baiwa William Ruto uziri na rashin halartar zaman kotun, idan bukatar hakan tana da matukar muhimmanci, a yayin sauraron tuhumar da ake masa a Shalkwatar kotun dake birin "The Hague na kasar Netherlands.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita:Umaru Aliyu