1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsara harkokin addinai a Jamhuriyar Nijar

Salissou Boukari SB
October 25, 2019

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar ta dukufa samar da dokoki da za su tsara tafiyar da harkokin addinai cikin kwaciyar hankali ba tare da wani ya tsangwami wani ba.

https://p.dw.com/p/3RwOV
Niger Agadez Innenstadt
Hoto: picture-alliance/Tuul/robertharding

Duk da cewa akwai zaman lafiya tsakanin addinai a Jamhuriyar Nijar, amma kuma babbar matsalar ita ce ta rashin dokokin shari'a da ke ba da damar shirya mutane yadda kowa zai yi addininsa ba tare da tsangwame ba. Gwamnatin ta farka daga barci sakamakon ganin irin matsaloli da ake fuskanta a wasu kasashe makwabta, inda wasu ke fakewa da addini domin yin abin da bai dace ba.

Kiristoci da Musulmai dai a Jamhuriyar Nijar na tare da juna tun lokacin da kasar ta samu mulkin kai, inda suke zaune ba tare da wasu matsaloli ba. Batun hulda tsakanin addinai batu ne da ke da saukin gaske, duk wani abin da ya taso ta bangaren addini, za ka samu akwai masu tsawatawa.

A wannan zaman taro wanda ministan cikin gida Bazoum Mohamed ya jagoranta an samu halartar jakadun kasashen waje, sarakunan gargajiya da sauran masu fada a ji a fanni addinai.