1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soma aiki da dokar tsaro a Hong Kong

Abdoulaye Mamane Amadou
July 1, 2020

Wasu manyan kasashen duniya na ci gaba da yin kakkausar suka game da dokar tsaron da China ta kakaba a yankin Hong Kong, wacce ta tanadi hukuncin daurin rai da rai ga wadanda aka kama da laifi.

https://p.dw.com/p/3ec5b
Hongkong | Carrie Lam spricht am Tag des 23 Jubiläum der Übergabe an China
Shugabar yankin Hong Kong Carrie LamHoto: Getty Images/A. Kwan

A ranar Talata 30 ga watan Yunin da ya gabata ne, dokar ta soma aiki gadan gadan biyo bayan majalisar dokokin China ta kada kuri'ar amincewa da ita, tare da bai wa kotun China damar zartar da hukunci ga wadanda aka kama da aikata mumunan laifi da ya saba dokar a yankin Hong Kong.

A yayin da take tsokaci game da sabuwar dokar a albarkacin ranar tunawa da sake komawar yankin a hannun kasar China, shugabar yankin Hong Kong Carrie Lam, ta yabawa sabuwar dokar da yanzu hakan ke ci gaba da haddasa cece-kuce, ta na mai cewa sabuwar dokar a matsayin wani sabon mataki da ka iya yin farraku da dagula al'amura na jagoranci na gari a yankin.