1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kafa dokar hana hawa babura a Zamafara

Abdoulaye Mamane Amadou
August 28, 2021

A wani mataki na rage radadin hare-haren 'yan bindiga da barayin shanu a Zamfara da ke yankin arewacin Najeriya, gwamnatin jihar ta yanke hukuncin hana bude kasuwanni da takaita hawan babura da safarar shanu.

https://p.dw.com/p/3zc3i
Nigeria Viehdiebstähle in ländlichen Regionen
Hoto: DW/Katrin Gänsler

Gwamnatin jihar Zamfara dake Arewa maso yammacin Najeriya ta sanya wasu dokoki a jihar da nufin magance matsalar tsaro da ta yiwa jhar dabaibayi. Matakin da ake ganin zai kasance mai tsauri na da niyar ne takaita yawaitar hare-haren da barayin daji da 'yan bindiga ke kaiwa fararen hulla tare da satar dukiyoyinsu a yankin.

A cikin wata hira da sashen hausa na DW, gwamnan Jihar Dr Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana jerin wuraren da dokar ta shafa da suka hada da kasuwanni da hawan babura da kasuwancin shanu da na itace da sauransu. Masana tsaro dai na ganin idan Al'umma sukai hakuri suka bi Dokokin to za'a samu saukin matsalar duba da yadda matsalar tsaron jihar ke neman ta gagari kundila.