Dokar hana fita a Liberia don yaƙi da Ebola | Labarai | DW | 20.08.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dokar hana fita a Liberia don yaƙi da Ebola

Hukumomin ƙasar Liberia sun ɗau matakai na ganin an magance saurin bazuwar cutar Ebola a tsakanin al'umma ta hanyar hana fitan dare.

Gwamnati ta ƙaddamar da dokar hana fitan daren a faɗin ƙasar, bisa matakan shawo kan bazuwar cutar ta Ebola. An kuma killace wasu anguwanni biyu cikin birnin Monrovia, inda wasu da ake jinya tun da farko suka tsere kafin a ganosu.

A halin da ake ciki Majalisar Ɗinkin Duniya na yin wani yuƙurin ganin ƙwararru masu kula da sha'anin kiwon lafiyar sun samu nasarar shawo kan bazuwar cutar ta Ebola a yammacin Afirka.

Mawallafi: Usman Shehu Usman Edita: Abdourahamane Hassane