1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dinke barakar Jamus da Turkiya

Usman Shehu UsmanSeptember 8, 2016

Ministan harkokin wajen Jamus ya bayyana cewa Turkiya ta amince wa 'yan majalisar dokokin kasar da su kai ziyara a sansanin sojojin kawance da ke Incirlik a kasar ta Turkiya.

https://p.dw.com/p/1JySY
Berlin Merkel Erdogan
Hoto: Imago/Zuma

Hukumomin Ankara dai tun gabanin juyin mulkin da aka so yi wa gwamnatin Recep Tayyib Ergogan, suka dau matakin hanawa, wasu 'yan majalisar dokokin Jamus kai ziyara a sansanin sojojin saman kasar, inda wasu sojojin Jamus ke zama. Kasar Jamus na da sojojinta a sansanin Incirlik cikin kasar Turkiya, inda suke cikin kawancen yaki da kungiyar IS a kasar Siriya. An ruwaito ministar tsaron Jamus Ursular von der Leyen tana mai cewa, har yanzu bamu fidda tsammanin ganin an bar 'yan majalisar Jamus sun kai ziyar don ganin sojojin nasu ba. "Ina fatan ganin tawagar 'yan majalisar mu da ke shirin kai ziyara a sansanin Incirlink a watan Oktoba, za a basu daman yin hakan" Dama dai Turkiya ta dau matakin hanawa 'yan majalisar dokokin Jamus ziyartar sanini ne, bisa fushin da ta ke yi da 'yan majalisar dokokin Jamus, wadanda suka kada kuri'ar amincewa. Armeniyawa da suka mutu a hannun Turkawa zamanin mulkin daular Othumaniya, ba komai bane illa kisan kiyashi, abinda ya harzuka dangantakar kasashen biyu.