Dilma Rousseff: juyin mulki ne aka yi min | Labarai | DW | 12.05.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dilma Rousseff: juyin mulki ne aka yi min

Shugabar Brazil da aka dakatar daga mukaminta ta danganta matakin da majalisu suka dauka da juyin mulki tare da shan alwashin wanke kanta daga zargn da ake yi mata.

Shugabar kasar Brazil da aka dakatar Dilma Rousseff ta yi alkawarin tsayawa a kan kafafunta wajen ganin ta wanke kanta daga zargin almundahana da majalisun kasar suka zargeta da aikatawa. Kwanaki 180 ita Rousseff take da su na kawo hujjojin da za su karya zargin da ake yi mata, ko kuma a tsigeta kwata-kwata daga kujerar mulki.

A wannan Alhamis ne 'yan majalisar dattawa suka bi sahun takwarorinsu na wakilai wajen kada kuri'ar amincewa da dakatar da Dilma Rousseff a matsayin shugaban kasar Brazil. Sai dai a lokaci da ta yi wa magoya bayanta jawabi bayan da fice daga fadar shugaban kasar, Dilma Rousseff ta danganta abin da ya faru da juyin mulki.

Ta ce " Idan zababben shugaba ya rasa mukaminsa kan laifin da bai aikata ba a kasa da ke bin tafarkin demokaradiyya, ana kiran wannan juyin mulki. babu wata kwakkwarar hujja ta dakatar da ni, ban tara kudi a kasashen waje ba, ban taba karbar na goro ba, ba ni da dangantaka da masu cin hanci da karbar rashawa."