1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Didier Drogba na neman shugabanci FIF

Mouhamadou Awal Balarabe AH
April 11, 2022

Didier Drogba zai kara da 'yan takara shida a zaben shugaban hukumar kwallon kafa na Côte d' Ivoire da za a yi a makon gobe.

https://p.dw.com/p/49mMr
Italien Monza| Ehemaliger Fußballspieler | Didier Drogba
Hoto: Imago Images

Tsohon dan wasan gaba na Côte d' Ivoire Didier Drogba ya yi nasarar tsayawa takarar shugabancin hukumar kwallon kafar kasarsa, bayan shafe lokaci na takun saka kan ka'idodin da ya kamata a cika wajen neman wannan mukami. Ita hukumar gudanarwar ta FIF da ke kula da kwallon kafa a Côte d' Ivoire ce ta sanar cewa 'yan takara shida ne a hukumance suka mika takardar neman shugabancin hukumar da aka shirya gudanarwa a ranar 23 ga watan Afrilu, ciki har da tsohon dan wasan Chelsea Didier Drogba, da Aka Arnaud, tsohon mataimakin shugaban hukumar FIF da Idriss Diallo da Sory Diabaté, tsohon mamba a kwamitin zartarwa mai barin gado da Konan Kouakou Laurent. Didier Drogba dai, duk da matsayinsa na tsohon tauraron dan wasan kwallon kafa na Afirka, ba lallai ne ya zama wanda zai kai labari a wannan zabe ba, saboda rashin samun isasshen goyon baya a tsakanin kungiyoyin Côte d' Ivoire. Amma ya kasance ficeccen dan wasan kwallon kafa na biyu cikin shekara guda da ke neman shugabancin hukumar kwalon kafar kasarsa ta haihuwa baya ga samuel Eto'o Fils na Kamaru da ya lashe zabe. An yi ta dage wannan zabe na hukumar kwallon kafar Côte d' Ivoire sau da yawa tun daga shekarar 2020, saboda rashn kyakkyawan tsarin tsayar da 'yan takara. Sai da ya kai hukumar kwlalon kafa ta duniya FIFA ta sanya FIF karkashin kulawarta a watan Disamba 2020 ta FIFA, tare da  kafa Kwamitin Daidaitawa don warware wannan rikicin. Wannan zabe na zuwa ne a daidai lokacin da Côte d'Ivoire ke shirin karbar bakuncin gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afrika a shekarar 2023.

 CAF ta dakatar da buga wasa a filin kwallon kasa janar Seini Kountche a Nijar

Niger Wahlen Kandidat Ibrahim Yacouba
Hoto: I. Sanogo/AFP/Getty Images

Hukumar kwallon kafa ta kasashen Afirka wato CAF ta sake daukar matakin dakatar da gudanar da wasannin kasa da kasa a babban filin kwallon kafa na kasar Nijar na janar Seini Kountche da ke a birnin Yamai, a bisa kasa cika sharudda da hukumar ta gindaya wa filayen wasanni. Tuni kuma ma’abota kwallon kafa a kasar suka soma kira ga mahukuntan kasar ta Nijar da su gaggauta daukar matakin shawo kann matsalar, lamarin da ya sa hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta kasar wato FENIFOOT ta yi bayani.

Faransa ta kafa sabon tarihin na yawan kwallaye da a aka zira a raga a gasar kwallon kafa ta kasar
Yanzu kuma sai fagen kwallon kafar kasashen Turai, inda Faransa ta kafa sabon tarihin na yawan kwallaye da a aka zira a raga sakamakon kwallaye 38 da aka samu a wasanni goma da aka shirya a mako na 31 na babban lig din kasar. Wannan ya zarta adadin kwallaye 35 da aka zira a cikin watan Janairu  a mako na 22. Hasali ma dai, kwallaye 20 da aka zira a wasanni uku farko, inda Lorient ta samu nasara da ci 6-2 a kan Saint-Etienne, sannan PSG ta yi kaca-kaca da  Clermont Ferrand co 6-1. Wannan ya sa Paris saint Germain ta fara jin kamshin kambun zakara tunda  tana gaban Marseille da maki 12. A gasar Premier ta Ingila kuwa, an yi kare jini biri jini tsakanin Manchester City da Liverpool da ke saman teburi inda aka tashi (2-2), lamarin da ya City ke ci gaba da yi wa Liverpool ratar maki daya, a daidai lokacin da ya rage wasanni bakwai akwai karshen kakar wasanni. Dama dai makamancin wannans sakamakon wadannan kungiyoyin suka samu a matakin farko na wasan da suka gudanar tsakaninsu.A La Liga na Spain kuwa, da kyar Kungiyar FC Barcelona ta tsira daga hannun #yar baya ga dangi Levante da da ci (3-2), a mako na 31 na. Luuk de Jong ne ya bai wa Barca nasara a mintunan karshe na wasan. Don haka Barcelona ta tsawaita jerin wasanninta bakwai cikin nasara a La Liga. Rabon dai a doke Bercelona tun sama da watanni hudu, a ranar 4 ga Disamba da  Betis Sevilla.

Champions League | RB Leipzig v Paris St Germain |   Leipziger Torewarts Peter Gulacsi
Hoto: Hartmut Bösener/imago images

Bayern Munich ta so ta yi amfani da wasan mako na 29 na Bundesliga wajen kara kwarin gwiwa

Bundesliga - Bayern Munich v FC Augsburg
Hoto: LUKAS BARTH/REUTERS

A nan jamus aski ya fara isowa gaban goshi a kokarin da kungioyyi kwallon kafar Jamus ke yi na zama zakaran Bundesliga, inda gudanar da wasannin mako na 29 da suka so dagula wa bayern lissafi. Bayern Munich ta so ta yi amfani da wasan mako na 29 na Bundesliga wajen kara kwarin gwiwa kafin ta kara da Villarreal a wasan daf da na kusa da na karshe na gasar zakarun Turai. Amma nasarar da ta samu da jibin goshi a kan Augsburg da ci 1-0, ba lallai ba ne ya kwantar da hankali ba, saboda Bayern Munich ta fuskanci duk wata matsala  wajen tika FC Augsburg da kasa. Sai da ja gaban ta jira minti 82 bayan da  Robert Lewandowski ya yi bugun fanareti tukuna ta zura daya dayan kwallo a raga.A cewar koci Julian Nagelsmann na Bayern, tawagarsa ba ta taka kyakkyawar rawa ba, amma hakarta ta cimma ruwa. Yanzu dole ne mu mai da hankali kan gasar zakarun Turai.“ Ban damu da yadda aka samu nasara ba. Abu mafi muhimmanci shi ne nasara kuma abin da muka yi ke nan. Ba mu kasance a matakin kakar wasan da ya kamata mu burge ba. Amma tabbas ba wasa mai kyau muka yi ba, ba mu samar da damammaki da yawa ba. Mun yi wasan jeka na yi ka, duk da cewa muna da sarari da yawa na wasa. Mun farfado bayan hutun rabin lokaci, inda muka yi matsin lamna na minti 15-20 da kuma minti goma na karshe da suka yi mana kyau. Augsburg kungiya ce mai kyau, kuma lokaci ne mai sarkakiya tsakanin haduwa da za mu yi da Villarreal. Muna da wasa mai mahimmanci a ranar Talata, don haka yana da mahimmanci mu samu nasara."