Kwas din harshe na "Deutsch - warum nicht?" yana ba da labarin Andreas, dalibi mai karantun aikin jarida, da ke aikin tsaron kofa a otal. Kowane jerin shirye-shirye ya kunshi darussa 26 tare da tattaunawa, ayyukan yi, da yankunan sautin da za a iya saukewa. Kwas din harshen ya hade matakai na A1 zuwa B1 na Ginshiken Turai na bai-daya na Mahangar Harsuna. An shirya shi don masu koyo a matakin farko da na gaba. An kirkiri "Deutsch - warum nicht?" ne da hadin gwiwar Goethe - Institut.
Matakai: AI, A2, B1
Midiya: Sauti, Rubutu (Saukarwa)
H arsuna: Jamusanci | Hausa