1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An bude yakin neman zab a Kwango Brazzaville

Abdourahamane Hassane
March 5, 2021

A ranar 21 ga watan Maris za a gudanar da zagaye na farko na zaben shugaban kasa a Kwango Brazzaville.

https://p.dw.com/p/3qHVE
Kongo Präsident Denis Sassou Nguesso
Shugaban Kasar Kwango Brazzaville Denis Sassou Nguesso Hoto: picture-alliance/AA/A. Landoulsi

An bude yakin neman zabe a Kwango Brazzaville a zaben shugaban kasar da za a gudanar a ranar 21 ga watan Maris wanda shugaba mai ci Denis Sassou Nguesso dan shekaru 77 wanda ya yi shekaru 36 a kan mulki, zai tsaya takara a wa'adi na hudu. A zaben da aka gudanar a shekara ta 2016 wanda Denis Sassou Nguesso ya samu nasara, tashin hankali ya barke bayan da 'yan adawa suka ce an yi aringizo a zaben.