1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dayton - shekaru 10

YAHAYA AHMEDNovember 21, 2005

A ran 21 ga watan Nuwamban shekara ta 1995 ne aka kulla yarjejeniyar Dayton, wadda ta share fagen samad da zaman lafiya a kasar Bosniya. To yau, shekaru 10 bayan haka, me aka cim ma ?

https://p.dw.com/p/Bu45
Shugabannin yarjejeniyar Dayton
Shugabannin yarjejeniyar DaytonHoto: AP

Abin yabo ga yarjejeniyar ta Dayton dai, shi ne ta kawo karshen masifar da da dimbin yawan jama’a ke sha a lokacin yakin na Bosniya. Ita ce ta janyo rushe kawanyar da aka yi wa birnin Sarajevo, har kuma aka sami damar kai wa mazauna birnin da ke fama da yunwa taimakon abinci da wasu kayayyakin agaji. Kazalika kuma, ta share fagen komawar `yan gudun hijira zuwa matsugunansu da suka kaurace wa a lokacin yakin. Bisa ka’idojinta ne kuma aka shirya zabe, har aka iya samad da kafofin dimukradiyya da na tattalin arziki a kasar ta Bosniya.

Yarjejeniyar ta Dayton, ta kuma yi farin jini a bainar jama’ar yankin Balkan ne, saboda ta bai wa duk al’ummomin yankin damar tuntubar juna a fannonin kabilu da na addinai. Ta kanta ne kuma aka sami dandalin tantance kurakuran da aka yi a baya, har aka iya gano gawawwakin wadanda aka yi musu kisan gilla a lokacin yakin, aka tabbatad da asalinsu.

Amma duk da wadannan fa’idojin da aka yi wa yarjejeniyar ado da su, masharhanta da dama na ganin cewa, ba a nuna adalci wajen zartad da ita ba. A daura da Jamus a la misali, inda bayan yakin duniya na biyu, aka fatattaki duk masu bin ra’ayin Nazi, a Bosniya ba haka lamarin ya kasance ba. An gina kafofin dimukradiyya ne a kan harsashen tsohon tafarkin nuna kyama da bambancin kabilu a yankin.

Ana dai sukar yarjejeniyar ta Dayton ne da kago wani sabon salo a Bosniyan, inda bisa ka’idar kabuilanci ne kawai, za a rarraba madafan iko a majalisa da kuma gwamnati. Wasu kuma na zarginta ne da kara haddasa kyama da bambancin addini da na kabilanci a makarantun kasar. Masu wannan ra’ayin na matashiya ne da cewa, a halin da ake ciki yanzu dai, madugan yakin ne kuma ke jan ragamar mulki a kasar ta Bosniya.

Hakan kuwa a nasu ganin, ya sa hukumomin kasar ba sa iya gudanad da aikinsu kamar yadda ya kamata. Akwai dai manyan kabilu guda biyu a kasar, da jihohi 10, da lardi daya, da gwamnatin tsakiya, da majalisu da gwamnatocin jihohi 14, inda kuma duk yawan al’umman bai fi miliyan 4 ba. Kazalika kuma, inji masu sukar yarjejeniyar, ba a gabatad da kundin tsarin mulkin kasar bisa tafarkin dimukradiyya ba. A Dayton aka amince da ita, ba tare da bai wa al’umman kasar damar ka da kuri’un yin amanna ko kuma watsi da shi ba. Wadanda suka sanya hannu a kanta don ta fara aiki dai su ne shugaban Serbiya, Slobodan Milosevic, da shugaba Franjo Tudjman na Croatia da kuma shugaba Alija Izetbegovic na Bosniyan.

Yanzu ko, kiran da ake yi, shi ne na bai wa al’umman kasar Bosniya-Hezegovina damar samar wa kansu kundin tsarin mulkin da ya dace, bisa adalci, wanda zai kau da duk wasu alamun kabilanci a kasar, ya kuma share mata fagen shiga cikin gamayyar Turai. Hakan dai ba zai yiwu ba, sai Turai da Amirka sun ba da ta su gudummuwa. Amma abin da ya fi muhimmanci ga al’umman kasar, shi ne su tashi tsaye da kansu, su yi hangen nesa wajen tsara wa kansu kyakyawar makoma, su kuma dau matakan aiwatad da duk wasu ka’idojin da za su yarje a kansu.