1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Daurin shekaru 9 kan matar da ta kashe jarirai biyu

Ramatu Garba Baba
April 5, 2018

Kotu a Jamus ta zartas da hukuncin zaman gidan yari na shekaru tara da rabi kan matar da ta kashe jariranta biyu jim kadan bayan haihuwarsu tare da boye gawarwakinsu don kaucewa fushin hukuma.

https://p.dw.com/p/2vXxu
Deutschland Prozess gegen Andrea G. vor dem Landgericht Coburg
Hoto: picture alliance/dpa/D. Karmann

Binciken ya gano yadda matar ta boye gawarwakin jariran biyu cikin na'aurar sanyaya abinci ko Freezer a turancin Ingilishi bayan ta aikata kisan da suka ce ta yi ne ta hanyar shake su har sai da suka daina numfashi.

Masu shigar da kara sun tabbatar da cewa Andrea G mai shekaru 46, ta na cikin hayyacinta a lokacin da ta aikata kisan biyu, daya a shekarar 2004 dayan kuma a shekarar 2008, amman lauyan da ke kare matar ya ce, mutumin da suke zama tare a matsayin mijinta a lokacin ne ya tursasa ma ta daukar matakin baya da ya ce baya son karin iyali baya ga biyun da suke da su.Yanzu haka an soma gudanar da bincike kan mutumin da ake zargi da masaniya kan kisan daya daga cikin yaran ba tare da ya sanar da hukuma ba.