Daurin rai da rai ga sojin Côte d′ Ivoire | Labarai | DW | 18.02.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daurin rai da rai ga sojin Côte d' Ivoire

Kotun da ke birnin Abidjan ta yanke hukuncin daurin rai da rai ga wasu sojoji uku bayan da ake samesu da laifin kashe tsohon shugaban mulkin sojan kasar Janar Robert Guei

Bayan zaman shari'a na tsawon watanni uku kotun ta samu sojojin uku da suka hada da komandan Anselme Seka Yapo tsohon dogarin Simone Gbagbo da aikata laifin kisa. Kotun ta kuma yanke hukuncin zaman kaso na tsawon shekaru goma-goma ga wasu sojojin shida daga cikin 19 da aka tsare kana ta saki sauran.

A ranar 19 ga watan Satumbar shekara ta 2002 ne aka kashe Janar Robert Guei dan shekaru 61 a lokacin wani yinkurin kifar da mulkin Shugaba Gbagbo da sojojin suka yi a birnin Abidjan .