1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fursunoni 800 sun kubuce wa gwamnatin Kwango

August 11, 2022

Hukumomi a Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango sun tabbatar da tserewar daruruwan fursunonin da ke tsare ciki har da tsagerun mayakan kungiyar ADF masu gwagwarmaya da makamai tare da kisan 'yan sanda biyu.

https://p.dw.com/p/4FPst
Felix Tshisekedi | Präsident Demokratische Republik Konogo
Hoto: Arsene Mpiana/AFP/Getty Images

Akalla mutane biyar ne aka tabbatar da mutuwarsu ciki har da 'yan sanda biyu a harin na gidan yari da bayanai ke tabbatar da tserewar daurarru akalla 800 daga gidan yarin Kwakwangura.

Lamarin da ya faru a garin Butembo na gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, an dora alhakin faruwar sa a kan mayakan tawaye na Allied Democrtic Forces, ADF.

Jami'ai sun ce maharan sun far wa gidan yarin ne lokacin da ake tafiya da wasu fursunoni, an kuma yi nasarar kone wasu uku daga cikin 'yan tawayen da suka kai harin.

Tsagerun na ADF, sun samu bayanai ne na cewa a ranar Laraba za a sauya wa wasu mata fursunoni da suke da alaka da su matsuguni zuwa wani jarum da ke birnin Beni.

Kakakin rundunar sojan yankin na Butembo da ke cikin ayarin da suka kai ziyarar da ya shaida abin da ya faru a gidan yarin, Anthony Mwalushay, ya bayyana abin da ya gane wa idanunsa

"Wadannan tsageru na ADF da suka fito daga kwarin Malika, sune suka yi nasarar fasa wannan babban gidan yari na Butembo da wannan ta’asar da suka tafka" in ji Mwalushay

Ko a cikin watan Oktobar 2020 ma dai wani hari da aka kai gidan yarin Kangbayi ya yi sanadiyyar tserewar fursunoni kimanin 1,300 a yankin Beni da ke a lardin Kivu da ke Kwangon.

Tuni dai kungiyoyin da ba na gwamnati ba, suka kara kira da babbar murya ga mahukuntan kasar ta Kwango da su sake dabarun karfafa harkokin tsaron a fadin kasar, musamman sama wa sojoji makaman yaki bayan faruwar lamarin na baya-bayan nan.

Sojoji a Kwangon dai sun ce kungiyar IS da mayakan ADF ke yi wa biyayya sun dauki alhakin harin na gidan yarin Kwakwangura. Kuma a ciki sun kubutar da mayakansu mata su 12 da ma wani shugaban kungiyar da ke a tsare.

Wasu daga cikin jami’an da ke aiki a gidan yarin, sun ce daga cikin mutum 872 da ake tsare da su a gidan, 49 ne kadai ba su tsere ba.