Dauki ba dadi tsakanin rundunar JTF da B/Haram | Siyasa | DW | 03.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dauki ba dadi tsakanin rundunar JTF da B/Haram

Wasu ‘yan bindiga da ake zaton ‘yan Kungiyar Boko Haram ne sun kona gidan gona na hukumar kula da gidan Yari a Maiduguri inda fursunoni da dama suke tsere.

Wannan hari ya biyo bayan fito-na-fito ne da ‘yan kungiyar a jihar Yobe inda aka samu hasarar rayuka. Mazauna kusa da wannan gidan gona dake kan hanyar Gamboru Ngala sun bayyana cewa maharan sun yi amfani da manyan bindigogi gami man fetur inda suka kona wasu ofisoshi da dakin shan magani da ma'aikatan gidan yarin ke amfani da su. Ana hasashen cewa maharan da ake zaton ‘yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram sun je kubutar da wasu mutanen su ne da ake zaton ana tsare da su a wannan gidan gona sai dai jami'an tsaro sun musanta hakan.

Kakakin rundunar tabbatar da tsaro ta JTF ta tabbatar da wannan hari sai dai tace kalilan daga fursunonin masu koyan sana'a ne suka tsere ba dadewa ba kuma wasun su suka dawo kuma rundunar su ta kai dauki na gaggawa da jin labarin harin.

Nigeria Polizei Polizisten auf Patrouille in Bauchi

Sintirin jami'an tsaro a biranen arewacin Najeriya

Masharhanta dai na ganin sabbin hare-haren bayan nan na da nasaba da kokarin da kungiyar ke na tabbatar da karfin bayan da hukumomin kasar ke shelar cin karfin su kamar dai yadda shugaban Jonathan ya bayyana har ma da cewa suna kame da manyan wadanda ke da hannu wajen tada bama-bamai a muhimman wurare a kasar. Malam Isma'il Abubakar wani mai fashin baki ne kan harkokin yau da kullum a Najeriya. Daga jihar yobe kuma an yi ba-ta-kashi tsakanin jami'an tsaro na JTF da ‘yan kungiyar Boko Haram a unguwar Yandiski da ke bayan garin Potiskum inda aka samu hasarar rayuka da dama.

Rundunar tsaro ta JTF ta tabbatar da wannan sabon fadan sai dai tace an kashe ‘yan kungiyar guda 4 da dan Sanda daya. Sai dai har yanzu Jama'ar kasar na ganin amfani da karfi ba zai magance wannan matsalar ba kamar yadda Adamu Adamu mai Dala ya shaida min. Yanzu haka kuma Rundunar tabbatar da tsaro da wanzar da zaman lafiya a jihar Borno ta yi zargin cewa boye ‘yan kungiyar Boko Haram da al'ummar jihar Borno ke yi da kuma rashin baiwa jami'an tsaro hadin kai shine ke zama babban kalubale ga kokarin shawo kan matsalar rikicin.

Bombenanschlag Nigeria

Hare-haren yan ta'adda sun zama ruwan dare

Kakakin rundunar Laftanar Kanar Sagir Musa wanda yayi wannan bayani yace sabanin sauran garuruwa kamar Kano da Kaduna inda al'umma ke kokarin taimakawa jami'an tsaro a jihar ta Borno babu wannan kokari shi ya sa ake ci gaba da yin kisan sunkuru da kuma ci gaba da samun tashe-tashen hankula. Saboda haka ya shawarci al'ummar jihar da su fito su bayyana masu kai hare-haren ta hanyar baiwa jami'an tsaro hadin kai da bayanai da zasu taimaka musu a ayyukan su.

Sai dai masharhanta da masana na ganin da wuya al'umma su fito su taimakawa jami'an tsaron saboda yadda ake zargin su da cin zarafin mutane kuma duk wanda ya taimakawa jami'an tsaro nana bi a kashe shi. Isma'il Yunusa wanda aka fi sani malam Kaka na cikin masu wannan fahimta. Saboda haka su ka bukaci jami'an tsaron da su kayautata dangantakar su da al'umma ta haka ne kawai zasu iya samun nasarar a ayyukan su.

Mawallafi: Al Amin Suleiman Mohammed
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin