Daukar matakan gaggawa a kan Ebola | Labarai | DW | 26.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daukar matakan gaggawa a kan Ebola

Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da wani taron gaggawa domin tattauna batun annobar cutar Ebola da ta addabi yankin yammacin Afirka.

Da ya ke jawabi a wajen taron shugaban Amirka Barack Obama kira ya yi da a dauki matakan gaggawa domin dakile cutar. A nasa jawabin shugaban bankin duniya Jim Yong Kim ya ce za a ware dalar Amirka miliyan 400 domin yakar cutar ta Ebola. Ita kuwa kungiyar likitoci na gari na kowa wato "Doctors without Borders" ta nunar da cewa cutar na shirin fin karfinsu. Shugabar kungiyar Joanne Liu ta shaidawa taron na Majalisar Dinkin Duniya cewa suna bukatar karin kayan aiki da magunguna. A kasar Saliyo kuwa daya daga cikin kasashen da annobar ta fi shafa an kebance wata anguwa da ke dauke da mutane sama da miliyan guda domin dakile yaduwar Ebolan.