Da kwasakwasan Jamusanci na kyauta daga Deutsche Welle, za ka iya zabar salon koyo da ya fi dacewa da kai: koyo ns kan intanet a kwamfuta, tare da gajerun bidiyo, kwasakwasan sautin murya ko podcasts, or tare da rubutu da takardun aiki da za ka iya fitarwa. Zabi daga kwasakwasan masu koyo a matakin farko, masu koyo na tsaka tsaki da kuma masu koyo da suka yi nisa. Masu koyar da harshen Jamusanci za su iya amfani da kayayyakin multimedia dinmu a darussan su. Mai nemo Kwas za ta taimaka maka ka zabi kyakkyawan tsari ga kowane mataki.