Daruruwan mutane na nuna fushinsu a Jordan | Labarai | DW | 06.02.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Daruruwan mutane na nuna fushinsu a Jordan

Mutane a kasar Jordan na zanga-zangar Allah wadai da kisan matukin jirgin kasar da kungiyar IS ta yi

Dubun dubatan mutane a Jordan sun yi dafifi a manyan titunan birnin Amman na kasar, inda suke ta Allah wadai da kisan matukin jirgi dan kasar Muath Al Kasasbeh da mayakan kungiyar IS suka halaka ranar Talatar da ta gabata.

Wannan gangamin dai na zuwa ne kwana guda da kasar ta Jordan ta ce jiragenta na yaki sun tarwatsa wani sansanin mayakan na IS da ke Syria, abin da ke zama martani ga kisar Mualth Al- Kasasbeh.

Masu zanga-zangar sun yi maci ne musamman a tsakiyar birnin na Amman dauke da foton marigayi Muath, suna tofin Allah-tsine ga kungiyar ta IS.

Ministan harkokin wajen kasar Nasser Judeh, ya shaidar cewa farmakin sojin kasar kan kungiyar ta IS, somin tabi ne.

Shi ma sarki Abdallah na II na Jordan ya sha alwashin cewa wadannan mayaka za su fuskanci yaki daga Jordan sakamakon aikin da suka aikata.