1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dare 9 a jere ana tarzoma a birnin Paris da kewaye

November 5, 2005
https://p.dw.com/p/BvMV
Duk da kiran da aka yi da a kwantar da hankali, an sake yin mummunar tarzoma a fadin kasar Faransa a daren jiya. A birnin Paris da kewaye kadai ´yan sanda sun ce an kone motoci sama da 220. Yayin da a unguwar Pierrefitte aka kwashe mutane kimanin 100 daga wasu gudaje biyu da aka cunna musu wuta. An kuma ba da rahotannin yin kone-kone a wasu birane na Faransa kamar a Rennes da kuma Nantes. Daukacin masu yin tarzomar da kone makarantun, kantuna da wuraren ajiye kaya ´ya´yan baki ne daga kasashen arewacin Afirka da na Afirka bakar fata wadanda suka dade suna cikin mawuyacin hali na talauci a Faransa. Ministan cikin gidan Faransa Nicolas Sarkozy ya kai wata ziyarar ba zata a wani caji ofis dake birnin Paris. Sarkozy ya sake yin zargin cewa wata kungiya ce ke rura wutar tashe tashen hankula.