Dangote shi ne ya fi kowa kuɗi a Afirka | Amsoshin takardunku | DW | 29.04.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Amsoshin takardunku

Dangote shi ne ya fi kowa kuɗi a Afirka

Alhaji Aliko Dangote ya mallaki zunzurutun kuɗi sama da Dalar Amirka miliyan dubu biyu.

Birnin Lagos cibiyar kasuwancin Aliko Dangote a Najeriya

Birnin Lagos cibiyar kasuwancin Aliko Dangote a Najeriya

A wani rahoto da mujallar Forbes ta 'yan Jari Hujja dake ƙasar Amirka ta fitar a watan Maris na wannan shekara da muke ciki ta bayyana Alhaji Aliko Dangote Attajirin nan ɗan Najeriya a matsayin wanda yafi kowa kuɗi a nahiyar Afirka. Ƙididdiga da mujallar ta forbes ta buga ya nuna cewar Alhaji Aliko Dangote ya mallaki zunzurutun kuɗi har Dalar Amirka Biliyan biyu da ɗigo daya.

Kuma wannan shine karo na uku da Attajirin mai shekaru 52 a duniya kuma ɗan Asalin jihar kano dake Arewacin Najeriya yake ɗaukan lamba ta ɗaya ta masu arzikin nayiyar afirka baki ɗaya.

Alhaji Aliko Dangote dai yayi fice ne wajen saye da sayarwa da kuma sarrafa siminti da Sukari da manfetur da dai sauran kayan masarufi na yau da kullum a ƙarƙashin kanfanin Dangote.

A yayinda kuma mutane irin su Micheal Otedola wani ɗan asalin Jihar lagos a Najeriya da Mo Ibrahim na Sudan amma mazaunin Birtaniya da Johann Rupert na Afirka ta kudu da Patrice Motsepe shima ɗan afirka takudun suke biya masa.

Haka kuma akwai Mohammed Al Amoudi na Habasha da kuma Nassef da Naguib Sawiris dukkannin su Misirawa da dai sauran su.

To sai dai kamar yadda malamin ya buƙaci sanin wanda yafi kuɗi a Najeriya, kawo yanzu babu wani ƙiyasi ko sunayen mutanen da sukafi kuɗi a Najeriya bayan shi Alhaji Aliko Dangote da Kuma Micheal Otedelon da ita wannan mujalla ta forbes ta buga.

Akasarin masu kuɗin da kake gani a Najeriya Hukumomi na duniya daban-daban basa sanya su cikin jerin masu kuɗi, a sabili da rashin bayanan kuɗaɗen su ko kuma dai ana ganin kuɗaɗen gwamnati ne da akayi sama da faɗi dasu.

Idan kuma aka taɓo irin wayanan mutane za'a ga akwai tsoffin shugabannin ƙasa da tsoffin gwamnoni ko kuma wasu manyan 'yan kasuwa da dai sauran su. To sai dai duk da haka Alhaji Aliko Dangote ya kasance shine mafi kuɗi a Najeriyan.

Mawallafi: Babangida Jibril

Edita: Muhammad Nasiru Awal