Dangantakar Jamus da Faransa ta cika shekaru 50 | Labarai | DW | 19.01.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dangantakar Jamus da Faransa ta cika shekaru 50

A dangane da bukin cika shekaru 50 na sanya hannu kan yarjejeniya Elysse ya ta tanadi kyauata dangankatar Jamus da Faransa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi kira da a kula da kara dankon zumuncinsu

A cikin wani jawabi da ta yi ta hanyar video Merkel ta ce babu wani au na tarihi da zi dawwama. . A don haka kowace zuriya na bukatar sabonta abubuwan na tarihi. Shugabarta gwamatin Jamus tace an kara samun kusantar juna takanin Jamus da Faransa ko da yake aka samu sabani rayi akan wasu batutua na muamman . Tace a don haka na bukatar neman shawarar juna domin karfafa danatakar kasashen biyu. A ranar 22 ga watan Janairun shekarar 1963 ne shugaba Charles de Gaule na faransa da shugaban gwamnatin Jamus Konrad Adenauer suka rattaba hannu kan yarjejniyar kawacem kasashen su biyu a fadar Elysee dake birnin Paris. A makon dake tafe ne majalisar dokokin ta Bundestag da majalisun zatarwar gwamnatocin biyu za su wani zama a birnin Berlin a dangane da zagoyowar wannan rana ta tarihi.

Mawalafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Yahhouza Sadissou Madobi