1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dangantakar Jamus da Afurka ta Kudu

April 27, 2004

Akwai kyakkyawar alaka tsakanin Jamus da Afurka ta Kudu duk kuwa da cewar a zamanin baya kamfanonin kasar ta Jamus sun kasance a cikin jerin kamfanonin ketare dake cin gajiyar tsarin mulkin wariyar jinsi kuma gwamnati ba ta fito fili ta yi Allah waddai da manufar ta banbancin launin fata a Afurka ta Kudu ba

https://p.dw.com/p/BvkE
Afurka ta Kudu shekaru 10 bayan kawo karshen mulkin wariya
Afurka ta Kudu shekaru 10 bayan kawo karshen mulkin wariyaHoto: UNICEF/Giacomo Pirozzi

Mahukunta da sauran al’umar Afurka ta Kudu sun ji zafin kudurin da aka yanke na ba wa Jamus damar karbar bakuncin wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya a harabar Jamus a maimakon ATK a shekara ta 2006, ko da yake mai yiwuwa kasar ta samu irin wannan dama dangane da shekara ta 2010. A lokacin da yake bayani game da haka ministan harkokin wajen jamus Joschka Fischer yayi nuni ne da cewar:

Wannan abu ne mai muhimmanci ga kasar Afurka ta Kudu. Ina iya fahimtar haka a matsayina na mai sha’awar wasan kwallon kafa. A sabili da haka zan yi murna da farin cikin ganin kasar ta samu wannan dama.

A lokacin wata ziyarar da ya kai ATK, Joschka Fischer ya sha nanata goyan bayansa a game da ba wa kasar damar karbar bakuncin wasannin kwallon kafa na cin kofin duniya. Wannan dama tana da muhimmanci ga kasar, wacce tuni ta zama ginshikin tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin kudancin Afurka. Amma fa Winrich Kühne, tsofon mashawarcin gwamnatin Jamus akan al’amuran ATK baya da irin wannan ra’ayi. A ganinsa kasar ATK bata da wani kakkarfan matsayi kuma ba ta da wata takamaimiyar kwanciyar hankali. To sai dai kuma duk da haka, kamar yadda Ushi Eid, karamar minista a ma’aikatar taimakon raya kasa ta Jamus ta nunar, ATK ita ce muhimmiyar kawar Jamus a nahiyar Afurka. Akwai kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu. Ita dai ATK yau kimanin shekaru goma ke nan da ta samu canjin manufofinta, daga mulkin wariyar jinsi zuwa tsarin zamantakewar demokradiyya. A wancan lokaci kuwa jam’iyyar the Greens ta kasance mai mummunar adawa da manufofin gwamnati. Domin kuwa ko da yake an samu daidaikun 'yan siyasa dake kyamar mulkin wariyar al’uma a ATK, amma ita kanta gwamnati ba ta cikin jerin kasashen dake wa ‚yan mulkin wariyar tofin Allah tsine. Daga cikin wadannan jami’an siyasa kuwa har da tsofon ministan harkokin wajen Jamus Hans-Dietrich Genscher, wanda a shekarar 1978, a cikin wani jawabin da ya gabatar a babbar mashawartar MDD yake cewar:

Wannan tsari na wariyar jinsi da banbancin launin bata ya saba da duk wata akida da nahiyar Turai tayi imani da ita. ATK kasa ce da ta kunshi jinsunan mutane dabam-dabam. Kasar zata samu zaman lafiya da kwanciyar hankali da kuma kyakkyawar makoma ne kawai idan girmama hakkin dukkan al’umarta tare da kamanta adalci tsakaninsu.

Amma abin takaici shi ne kasancewar tsofuwar gwamnatin Jamus ba ta hana zuba jarin kamfanonin kasar a ATK ba. Bugu da kari kuma ta sha bayyana dari-dari wajen biyayya ga matakan takunkumi na kasa da kasa da ake dauka domin karya tattalin arzikin ATK. A yanzun dai al’amura sun canza kuma akwai kakkarfan kawance tsakanin kasashen biyu, saboda babu wani mummunan tabo da tsofuwar alakar tare da gwamnatin wariya ta haddasa.