1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

120908 Dialog Christen und Muslime in Frankreich

Hillmann, Margit September 25, 2008

Manyan addinai a Faransa su ne Kirista da Musulunci. Ana kira da kyautata dangantaka tsakani.

https://p.dw.com/p/FOb0
Shugaba Nicolas Sarkozy da Paparoma Benedict na 16 a Paris.Hoto: AP

A farkon makon jiya fafaroma Benedikt na 16 ya kammala ziyararsa ta farko a Faransa tun bayan zaɓansa a matsayin shugaban mabiya ɗarikar Katholika na duniya. A bukukuwan addu´o´i da ya jagoranta yayin wannan ziyara a Faransa Paparoma ya yi kira da a bawa addinai damar taka muhimmiyar rawa a cikin al´umma. Ya ce ya kamata a sake sabon tunani ga manufar raba addini da siyasa. Gabanin ziyarar ta Paparoma an yi ta zargin shugaban Faransa Nikolas Sarkozy da wuce gona da iri bisa furuce-furuce da yake yi game da imaninsa da ɗarikar Katholika, inda masu sukar sa suka ce haka na yin barazana ga wanzuwar zaman lafiya tsakanin mabiya addinai daban daban a cikin ƙasar. To ko yaya dangantaka take tsakanin manyan addinan ƙasar biyu wato Kirista su miliyan 46 da musulmi kimanin miliyan huɗu a ƙasar ta Faransa? To in kun biyo mu a hankali za ku ji cikakken bayani a cikin shirin na yau wanda kamar kullum ni MNA zan gabatar.

A jawabin da yayi a fadar gwamnati ta Elysee lokacin ziyararsa ta farko a Faransa, Paparoma Benedikt na 16 ya ce ko da yake raba tsakanin addini da siyasa yana da muhimmanci ga ´yancin tafiyar da addini da tabbatar da nauyin da ya rataya kan ƙasa amma a lokaci ɗaya ya zama wajibi a fayyace rawar da addinin ke takawa wajen samar al´umma kyakkyawa. Shugaban na mabiya ɗarikar Katholika a duniya ya goyi da bayan shawarar shugaban Faransa Nikolas Sarkozy game da samun cikakken haɗin kai tsakanin siyasa da addini.

Shi dai shugaba Sarkozy yana shan suka game da fitowa fili da yake yi yana nuna matsayinsa na mai bin ɗarikar Katholika sau da ƙafa. Masu sukar lamirinsa sun ce da kamata yayi shugaban ya yi takatsantsan dangane da furuce-furucen sa domin hasali yana matsayin wakilin dukkan addinai da ma waɗanda ba su bin wani addini a ƙasar ta Faransa. Suka ce shugaban na barazana ga kyakkyawan tsarin zamantakewa wanda zai iya haddasa gaba da ganin ƙyashin juna da yin gogayya tsakanin dukkan al´ummomin ƙasar.

Myriam Bouregba mai magana da yawun ƙungiyar SERIC da ke zama wani dandalin tuntuɓar juna tsakanin musulmi da kirista a Faransa ta ce har yanzu ana rashin wata tattaunawa sahihiya tsakanin musulmi da kirista na ƙasar.

Myriam: “Ko da yake ana musayar ra´ayoyi tsakanin Kirista da Musulmi a fannin rayuwa ta yau da kullum wato kamar a wuraren aiki, tsakanin iyaye mata dangane da makarantun yaransu da kuma tsakanin yara da matasa waɗanda ke zuwa makarantu da jami´o´i ɗaya. To amma ba wata gagarumar tattaunawa da ake yi a ɓangarori masu muhimmanci da suka shafi hulɗar dangantaku tsakanin al´ummomin Kirista da Musulmi wato kamar batutuwa na addini da zamantakewa tsakani. Kiristocin sun san musulmi na yin azumin watan Ramadana kuma ba sa cin naman alade, amma in ban da shi ba su da wata masaniya game da addinin musulunci. Hakan nan su ma musulmin masaniyarsu ga addinin Kirista da al´adun kirista sama-sama ce kaiwa.”

Tun kimanin shekaru takwas da suka wuce ita dai ƙungiyar SERIC dake samun kuɗaɗen tafiyar da aikinta daga ƙungiyar tarayyar Turai da wasu cibiyoyin Kirista da Musulmi ta ke shirya tarukan ƙarawa juna sani tsakanin Kiristoci da Musulmi a faɗin ƙasar Faransa. A ƙarshen watan Nuwamban kowace shekara ƙungiyar ta na gayyatar al´umomin musulmi da kirista zuwa wani babban taro musayar ra´ayoyi da al´adu don inganta zamantakewa tsakani.

Ba ƙaramin aiki ba ne ƙoƙarin wayar da kan mabiya wani addini game da dokoki ko al´adun wani addini daban. Hakazalika a Faransa ba abu ne mai sauƙi ba faɗakar da mabiya addinai kamar Kirista da Musulmi da zumar ƙarfafa musayar al´adu tsakanin ƙungiyoyin addinan guda biyu. Ayyukan tarzoma da saka manufofin siyasa a cikin ayyukan addinan sun bar babban tabo a tsakani.

A cikin shekarun baya bayan nan rashin yarda da ƙyamar addinin musulunci da musulmin ƙasar ta Faransa ya ƙaru inji Myriam Bouregba mai magana da yawun ƙungiyar ta SERIC. Ta ce ´yan siyasa masu neman suna musamman masu danganta ayyukan tarzoma, tsattsauran ra´ayi da addinin musulunci da muslumi ke da laifin wannan mummunan yanayin da aka shiga. Ta ce su ma kafofin yaɗa labaru na da na su laifin wajen janyo rashin yarda tsakanin mabiyan manyan addinan biyu.

Myriam: “Hanya mafi dacewa ita ce ta amfani da kafofin yaɗa labaru kamar telebijin da gidajen rediyo. Domin ´yan jaridar Faransa ba sa yin adalci yadda ya kamata a rahotannin da suke bayarwa game da addinin musulunci, wanda hakan ke ƙara dagula wannan batu wanda a da ma yake da sarƙaƙiya. Kafofin yaɗa labaru a Faransa suna taka rawa wajen janyo rashin yarda da ƙaruwar banbancin da ake nunawa musulmin ƙasar.”

A daura da haka sannun a hankali musulmin na ƙara jin tamkar ana mayar da su saniyar ware da nuna musu wariya. Suna ƙorafin cewa har yanzu musulmi ko da kakaninsa na riƙe da fasfunan Faransa ne ana yi musu kallon ´yan ƙasa masu daraja ta biyu. Hakazalika suna fama da matsalolin wurin samun aikin yi da gidan zama. Suna sukan ´yan siyasa da ƙoƙarin hanawa musulmin ´yancin tafiyar da addininsu ta hanyar kafa wasu dokoki musamman dokar nan da ta hana ɗaura ɗan kwali a makarantu.

Bugu da ƙari mafi yawan musulmin ƙasar ta Faransa na zargin ´Yan siyasa da manyan ma´aikatan gwamnati da gindaya tsauraran dokoki don hana gina masallatai. Suka ce yayin da hukuma ke tallafawa kiristoci wajen gina wuraren ibadarsu su kuwa musulmi ba su da wata damar samun taimakon gina masallatai daga gwamnati. Sun dai yi nuni da tsarin raba addini da siyasa wanda ya haramta gwamnati shiga kowane irin aiki da ya shafi addini.

Duk da haka dai Myriam Bouregba ta ƙungiyar SERIC wadda ita kanta muslma ce na mai ra´ayin cewa tsarin ƙasar na babu ruwanta da addini shi ne hanya mafi dacewa wajen samun kyakkyawar zamantakewa tsakanin Kirista da Musulmi tare da ba da kariya ga tsirarun mabiya addinai a Faransa kamar musulmi.

Myriam: "Tsarin raba addini da siyasa dake aiki yanzu a Faransa na makantar da gwamnati wajen gane ainihin addinin da ´yan ƙasarta ke bi. Gwamnati dai tana ɗaukarsu a matsayin ɗaiɗaikun mutane maimakon ´ya´yan wata gamaiyar ta addini.”

Har yanzu dai babu wani kyakkyawan tasiri da aka gani dangane da shirin da majami´ar Katholika a Faransa ke ƙara nunawa don ƙarfafa tuntuɓar juna tsakaninta da wakilan musulmi. Suka ce kalaman da Paparoma ya taɓa yi a garin Regensburg game da tashe tashen hankula cikin addinin musulunci har yanzu abin na kara ciwa musulmin Faransa tuwo a ƙwarya. Suka ce a ziyarar da ya kai birnin Paris Paparoma Benedikt ya tattauna kai tsaye da wakilan ɗarikar Protestant da na gamaiyar Yahudawa amma ban da na musulmi. Suka ce gayyatarsu kaɗai aka yi haɗe da wasu ƙungiyoyin jama´a na Faransa ammam ba matsayin na addini ba.