Dangantaka tsakanin China da Afirka | Siyasa | DW | 02.05.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Dangantaka tsakanin China da Afirka

China ba ta tsoma baki a harkokin cikin gidan nahiyar Afirka a huldodin kasuwanci tsakanin sassan biyu.

Shugaba Hu a Kenya

Shugaba Hu a Kenya

Ziyarar kwanaki 10 da shugaban na China ya kai kasashen Marokko, tarayyar Nijeriya da kuma Kenya na da nufin inganta manufofin China a wannan nahiya. A cikin shekaru 10 da suka wuce harkar kasuwanci tsakanin China da Afirka ta rubanya har sau 10 musamman dangane da manufar da China din ke bi a Afirka, wato bambamtawa tsakanin harkar kasuwanci da siyasa. Rashin tsoma bakinta a harkokin cikin gidan kasashe ya taimaka bisa manufa.

Yanzu dai harkokin kasuwancin Afirka sun koma hannun China musamman saboda saken da nahiyar Turai ta yi wajen kulla huldodin cinikaiya masu ma´ana da wannan nahiya saboda dalilai na rashin kwanciyar hankalin siyasa. Rashin kwanciyar hankali a yankin Golf da sauran kasashen Larabawa ya sa ana saka ayar tambaya game da kafofin samun makamashi nan gaba. Ba ma ga China kadai ba, wadda a kullum bukatar ta ta makamashi ke karuwa. Yanzu haka dai China na samun rubu´in yawan mai da take bukata daga Afirka, kuma hakan na karuwa. Huldar tattalin arziki tsakanin kasar da Afirka ta fi karfi a fannin man fetir, inda ta fi sayen mai din daga Angola da kuma Sudan. A halin da ake ciki kasar ta fara fadada yawan man da take saya daga tarayyar Nijeriya.

Mulkin demukiradiya da gwamnatoci masu adalci shi ne sharadin da kasashen Turai da Amirka ke gindayawa a manufofinsu na zuba jari a Afirka. Kyakkyawan misali a nan shi ne yarjejeniyar da aka kulla kwana-kwanan nan tsakanin Chadi da Bankin duniya wadda bankin ne ya zana ka´idojinta. China kuwa ba ruwanta da bin wasu manufofi masu daure kai dangane da Afirka. Wato ba ta hada kasuwanci da siyasa, ba ruwanta da batutuwan da suka shafi kare hakkin Dan Adam ko tace labaru a wannan nahiya.

To sai dai haka wata manufa ce ta son kai. Domin tufafin da China din ke sakawa na kassara harkokin kasuwannin auduga a Afirka musamman tsakanin talakawa. Hakazalika jarurrukna da China gwamnatin Beijing ke zubawa a Afirka na taimakawa gwamnatocin mulkin kama karya ne kamar shugaba Mugabe na Zimbabwe. Wani abin bakin ciki kuma shi ne makamai da China ke sayarwa na kara rura wutar rikice-rikice a Afirka. Alal misali a cikin shekarun 1990 kasar ta sayarwa gwamnatin mulkin sojin Nijeriya da makamai. Sannan har yanzu tana sayarwa gwamnatin Sudan makamai wadanda ake amfani da su a yankunan kasar da ake fama da rikici a cikinsu. ´Yan tawayen Chadi da kuma ´yan Janjawid a yammacin Sudan dukkansu da makamai daga China suke aikata ta´asa.

Yayin da kasashen Turai ke kokarin ganin an samu gwamnatoci masu adalci da shimfida sahihiyar demukiradiya a Afirka, China kuwa tana bin manufofi ne na son kai. Wai shin mai yasa wata gwamnati a Afirka zata yi adalci ko amfani da kudaden raya kasa don yakar talauci, yayin da a cikin sauki zata samu kudi da sauran kayayyakin raya kasa daga China?

Yanzu lokaci yayi da ya kamata Turai ta canza salon tunaninta game da Afirka, wato ta daina kallon ta tamkar wata matalauciyar nahiyar. Kamata yayi ta san da cewa Afirka mai tarin albarkatun kasa ta na da muihimmanci.

 • Kwanan wata 02.05.2006
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu0N
 • Kwanan wata 02.05.2006
 • Mawallafi Mohammad Nasiru Awal
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink https://p.dw.com/p/Bu0N