Dangantaka ta yi tsami tsakanin Venezuela da Colombia | Labarai | DW | 26.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Venezuela da Colombia

Ƙasar Venezuela ta katse hulɗar diplomasiya da maƙwabciyarta Colombia. Venezuela ta ɗauki wannan mataki ne bayan da shugaban Colombia Avaro Uribe ya janye izinin da ya bawa shugaba Hugo Chavez a matsayin mai shiga tsakani na yin sulhu da ´yan tawayen FARC. Colombia na zargin cewa shugaba Chavez ya na son wuce gona da iri a tattaunawar da yake yi da ´yan tawaye. Tun a karshen watan agusta shugaban na Venezuela ke koƙarin ganin an sako wasu mutane da ´yan tawayen ke garkuwa da su to sai dai kawo yanzu babu wani sakamako na a zo a gani da ya samu.