Danganta tsakanin Jamus da Ruwanda ta inganta | Labarai | DW | 28.10.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Danganta tsakanin Jamus da Ruwanda ta inganta

A 'yan shekarun nan huldar kasuwanci tsakanin Jamus da Ruwanda ta yi kyau, inda yawan kamfanonin Jamus a Ruwanda ya ninka daga hudu zuwa 15.

Deutschland Louise Mushikiwabo bei Conflict Zone in Berlin

Louise Mushikiwabo ministar harkokin wajen Ruwanda

Kasar Ruwanda ta nuna bukatar fadada huldar dangantaka da fahimtar juna da Tarayyar Jamus. Ministar harkokin wajen kasar ta Ruwanda Louise Mushikiwabo ta nunar da haka a wata ganawa da ta yi da takwaran aikinta na Jamus Frank-Walter Steinmeier a birnin Berlin.

"Wannan lokaci ne muhimmi ga Ruwanda, saboda haka muka yanke shawarar cewa Ruwanda da Jamus za su ci gaba da tafiya tare ta hanyar inganta dangantaka tsakaninsu. Ina farin ciki da ci gaban da aka samu a huldar tattalin arziki, inda a cikin shekaru biyu da rabi yawan kamfanonin Jamus da ke aiki a fannoni daban daban a Ruwanda ya ninka daga hudu zuwa 15."

Shi kuwa a nasa bangaren ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier damuwa ya nuna da halin rashin tabbas a fagen siyasar kasar Burundi makociyar Ruwanda.

"Mun damu da dambarwar siyasa a Burundi, da ta fara samun kwanciyar hankali bayan shekaru gommai na yakin basasa. Sai dai kamar yadda takwarar aiki daga Ruwanda ta nunar ba za a samu rikicin kabilanci a Burundi ba."