1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dandalin Matasa: Zaman majalisa ko dakali

Waziri (Hon.)January 9, 2020

Ana danganta wannan zaman majalisa da rashin aikin yi da ya yi yawa tsakanin matasa, sai dai wasu na masu ra'ayin cewa kamata ya yi matasan kan su, su tashi haikan wajen cire wa kansu kitse daga wuta.

https://p.dw.com/p/3VwXA

A Najeriya musamman a arewacin kasar, matasa da ba su da aikin yi, sun rungumin tabi'ar nan ta zaman majalisa ko dakali, inda suke kwashe tsawon yini har zuwa cikin dare suna hira yawanci marasa amfani ga rayuwarsu. Ana danganta wannan zaman majalisa da rashin aikin yi da ya yi yawa tsakanin matasa, sai dai wasu na masu ra'ayin cewa kamata ya yi matasan kan su, su tashi haikan wajen cire wa kansu kitse daga wuta, tun da hukumomi sun gaza.