1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dandalin Matasa: Yunkurin tallafa wa tattalin arziki

January 23, 2020

Rikicin jihar Zamfara ya fi shafar mata da kananan yara, da hallaka masu mazaje musamman mazauna karkara, hakan yasa matasa maza da mata a jihar suka daura damarar bada gudumawar kawo karshen matsalar tsaro.

https://p.dw.com/p/3Wjaz
Matasan Zamfara masu bada gudunmawar tsaro
Matasan Zamfara masu bada gudunmawar tsaroHoto: DW/Y. Ibrahim

Matasa a jihar Zamfara da ke arewa maso yammacin Nigeria na taka muhimmiyar rawa wajen bada gudumawa dan kara dakile matsalar tsaro da ta yi wa jihar tarnaki tsawon lokaci, gami da yinkurin da suke yi na tallafa wa, dan farfado da dattalin arzikin jihar, wanda akwai akasin da za'a iya fuskanta, idan wannan yunkuri nasu ya gagara samuwa.