Dandalin Matasa 15.04.2021 | Zamantakewa | DW | 15.04.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Dandalin Matasa 15.04.2021

Bambancin amfani da kafofin sada zumunta a tsakanin watannin 11 na baya da na watan Azumin Ramadan da Musulmi ke son karin kusanci da Allah madaukaki.

Saurari sauti 09:52

Sanin kowa ne, cewa ana amfani da shafukan Facebook da WhatsApp da sauransu wajen kyauta ma'amala da jama'a da tofa albarkacin baki dangane da lamura dabam-dabam. To amma me ke banbanta amfani da kafofin sada zumunta na zamani tsakanin watannin 11 na baya da na watan azumi don samun kusanci da Allah subhanah wa ta'allah?

Ba a raba matasa da latse-latsen waya ko ma da a lokacin azumin watan ramadana ne, don ta haka ne suke tattauanwa kan abubuwan da suka shafi kwallon kafa ko fina-finai ko ma kayan kwalliya da bukukuwa. Sai dai Musulmi daga cikin su na surkawa da abin da ya shafi addini da al'amuran rayuwa don samun albarkar da ke cikin wannan wata mai alfarma.

Sai dai sabo da wasu masu jin jini a jika suka yi da kafofin sada zumunta na zamani ba ya sa, su juya musu baya kwata-kwata a watan Ramadana. Salahudden Muhammad da ke da zama a Kadunan Najeriya, ya ce yana samun nitsuwa wajen kyautata ma'amala da kowa, da sauran tafsiri da ma yada shi ta kafar Whatsapp, amma kuma wannan ba ya hana shi amfani da kafofin sada zumuntan wajen nishadantra da shi a fannin motsa jiki.