1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan takarar Trump ya sha kaye a zabe

Gazali Abdou Tasawa
December 13, 2017

Dan takarar jam'iyyar adawa ta Democrate Doug Jones a Amirka ya kafa bajintar kayar da dan takarar jam'iyyar Republicain na kusa da Shugaba Donald Trump Roy Moore a zaben 'yan majalisar dattawa a cikin jihar Alabama. 

https://p.dw.com/p/2pFi0
Alabama Senats-Nachwahl Wahlen Doug Jones
Hoto: picture-alliance/AP/J. Bazemore

Doug Jones ya lashe zaben ne da kashi 49,5%  a yayin da Roy Moore ya samu kashi 48,8%. Sai dai kuma Roy Moore ya bayyana cewa bai amince da wannan sakamakon ba ya zuwa yanzu, kasancewa tazarar da aka ce ya sha kayen da ita ba ta taka kara ta karya ba.

Wannan dai shi ne karo na farko a shekaru 25 na baya bayan nan da wani dan takarar jam'iyyar Democrate ya samu kujerar Sanata a wannan jiha ta kudancin kasar ta Amirka. 

Nasarar da Doug Jones ya samu kan Roy Moore wanda da ma ake zargi da yin mugun wargi da kananan 'yan mata, na a matsayin wani babban komabaya ga Shugaba Donald Trump da kansa.

Sai dai kuma duk da kayen da makusancin nashi ya sha a zaben, a shafinsa na Tweeta  Shugaba Trump ya yi wa Sanata Doug Jones barka kan nasarar da ya samu a wannan zabe .