Dan takarar jam´iyar PDP Umar Musa ´Yar Aduwa na nan lafiya garau | Labarai | DW | 07.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Dan takarar jam´iyar PDP Umar Musa ´Yar Aduwa na nan lafiya garau

Bayan jita-jitar da aka yi ta yadawa yau a kafofin yada labarun Nijeriya cewar dan takarar shugabancin kasar karkashin tutar jam´iyar PDP, ya rasuwa, ofishin kamfen din sa ya fid da wata sanarwa wadda a ciki ya ce Alh. Umar Musa ´Yar Aduwa yana nan lafiya garau. Ofishin ya ce Musa ´Yar aduwa wanda kuma shine gwamnan jihar Katsina zai ci-gaba da kasancewa dan takarar jam´iyar PDP a zaben shugaban Nijeriya da zai gudana a cikin watan afrilu. A jiya aka kawo Alh. Musa ´Yar Aduwa a wani asibiti dake nan Jamus don duba lafiyar sa, kuma nan gaba kadan zai koma Nijeriya don ci gaba da yakin neman zabe.