1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Dan jaridar Afirka ta Kudu ya kubuta daga IS

Abdul-raheem Hassan
January 3, 2020

A shekarar 2017 kungiyar IS ta yi garkuwa da dan jaridar Mohammed bayan da shiga kasar Siriya domin daukar hotunan barna da yakin kasar ya haddasa.

https://p.dw.com/p/3VhB3
Syrien März 2019 | IS-Kämpfer in Baghouz
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Aamaq News Agency

Shiraaz Mohamed dan jaridar Afirka ta kudu mai daukar hoto ya tsira dakyar daga hannun maykan IS bayan shafe shekaru uku a tsare a kasar Siriya.

Kafofin yada labaran Afirka ta Kudu sun tabbatar da cewa dan jaridar ya tsira ne da tallafin jami'an leken asirin  kasar Turkiyya. Sai dai gwamnatin Shugaba Cyril Ramaphosa na kasar Afirka ta kudun ba ta ce komai kan labarin ba, amma rahotanni na cewa gwamnatocin biyu sun dau lokaci suna tattaunawa kan ceto dan jaridar.