1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mutum uku sun mutu a harin Denmark

Ramatu Garba Baba
July 4, 2022

Kasar Denmark ta fada cikin jimami bayan da wani dan bindiga ya bude wuta a wasu rukunin shaguna a birnin Copenhagen inda nan take ya hallaka mutum akalla uku.

https://p.dw.com/p/4Dbai
Dänemark Kopenhagen Schüsse in Einkauszentrum Fields
Hoto: RITZAU SCANPIX via REUTERS

Jama'a na cikin tashin hankali bayan wani hari na kan mai uwa da wabi da wani matashi ya kai kan rukunin kantuna da ke a Copenhagen babban birnin kasar Denmark. Kawo yanzu, mutum uku aka iya tabbatar sun mutu a yayin da wasu da dama ke asibiti kwance, cikin mawuyacin hali.

Tuni aka cafke maharin da aka ce, dan shekaru ashirin da biyu da haihuwa ne, ana kuma shirin gurfanar da shi a gaban kotu a wannan Litinin. Ba a dai kai ga tantance dalilin matashin na kai wannan harin ba ko sanin adadin wadanda ya halaka, a cewar babban sufeton yankin Soren Thomassen a jawabinsa ga manema labarai.