1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar karin kudin kaya bayan karin albashi

Nasir Salisu Zango GAT
October 31, 2018

A Najeriya 'yan kasuwa da sauran jama'a sun nuna damuwa a game da yiwuwar karin farashin kayayyakin masarufi bayan amincewar da gwamnonin jihohin kasar suka yi na biyan Naira dubu 22 a matsayin albashi mafi karanci.

https://p.dw.com/p/37UKM
Nigeria Menschenhandel Bundesstaat Benue
Hoto: DW/K. Gänsler

A Najeriya dai a duk lokacin da aka yi maganar albashi ga ma'aikata, babban abin da ke bijirowa ga wadanda ba ma'aikata ba shi ne batun tsadar kayan masarufi. Wannan karon ma ba ta sauya zani ba domin tun bayan da gwamnonin jihohin Najeriya suka amince da biyan Naira dubu 22 a matsayin sabon karin albashi, yan kasuwa da sauran masu sana'o'i suka fara kukan cewar kayan masarufi za su yi tsada, tun ma kafin a zo ga maganar amincewar 'yan kwadagon a kan wannan batu. 

Nigeria Abuja Markt in Gwarinpa
Hoto: picture-alliance/dpa/G. Esiri

Auwalu Muhamad wani dan kasuwa a Kano kuma mamba a kusa a kungiyar 'yan kasuwa ta Amata, ya ce babban abin yi shi ne a sami ingantaccen tsari matukar ana da muradin cin gajiyar wannan kari musmaman lakari da cewar akwai yiwuwar samun hauhawar farashi.
Shi kuwa Bashir Hayatu Jantile dan siyasa a jihar Kano cewa ya yi babban abin da ke ba shi mamaki da 'yan kwadago shi ne yadda suke kasa tabuka komai wajen tursasa gwamnati a kan batun ci-gaban alumma, sai dai kullum muradinsu shi ne na neman karin albashi kawai.

Nigeria Tomaten auf dem Markt in Port Harcourt
Hoto: DW/M. Bello

To sai dai a daidai lokacin da wasu 'yan Najeriyar ke korafi dangane da yiwuwar harhawar farashin kayayyakin masarufi a sakamakon karin albashin, Abubakar Saddik masanin tattalin arziki kuma mai fashin baki kan al'amuran yau da kullum, na ganin karin albashin wannan babban abin alkhairi ne domin ko ba komi zai amfani kowa domin arziki zai kewaya kowa ya samu.