Damuwa kan rikicin kabila da kagame | Labarai | DW | 14.09.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Damuwa kan rikicin kabila da kagame

Kungiyar SADC ta yankin Kudancin Afitka ta nuna fargabarta kan takun saka tsakanin shugabannin Ruwanda da kuma Jamhuriyar Demokaradiyyar kwango da ke gaba da juna.

Kasashen yankin kudancin Afirka sun nuna damuwarsu dangane da yadda kasar Ruwanda ke kara yawan sojojinta a kan iyakarta da Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango. Wata sanarwa da kungiyar ta SADC ta fitar, ta bayyana cewa mambobinta sun bukaci kasashen da ke makwabtaka da su taimaka wajen kawo zaman lafiya da tsaro da kuma kwanciyar hankali a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango.

A karshen watan da ya gabata dakarun kasar Kwango tare da na Majalisar Dinkin Duniya, suka kaddamar da hari a kan 'yan tawayen M23 a arewacin kasar. Sai hukumomin Kigali sun zargin takwarorinsu na Kinshasa da amfani da wannan dama wajen tsokanatsu da fada ta hanyar harba masu bama-bamai.

Majalisar Dinkin Duniya dai ta dade tana zargin Ruwanda da mara wa 'yan tawayen M23 bayan zargin da Ruwandan ke ci gaba da musantawa. Ana sa ran za a koma kan teburin sulhu tsakanin 'yan tawayen da gwamnatin kasar Kwango a ranar Talata mai zuwa bayan da aka samu tsaiko tun a watan Mayun da ya gabata.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe